Friday, October 27, 2023
TASHIN DOLLA DAKUMA FADUWAR NAIRA
Meye yake kawo tashin dollar a Nigeria 🇳🇬?
Masani ilimin tattalin arziki sun bayyana cewar, kusan kashi 80% cikin 100% na kayan da Nigeria take amfani dasu kayan kasashen waje kuma da dollar ake siyo su. Kusan danyan man fetir ne kadai Nigeria take futa da shi kasar waje wanda ake biyan ta dollar, sannan kuma itama ta bada maqudan dollars domin abata tatatcen man.
Atadalilin tabarbarewa ilimin primary, Secondary, dakuma university a Nigeria, ya zamanto masu kudi da masu riqe da madafun iko a Nigeria 🇳🇬 yayan su a kasashen waje suke karatu, kuma mafi yawan makarantun da suke zuwa a England, America, Dubai dakuma sauran kasashen duniya duk da dollar ake biyan kudaden makarantun.
Fanin neman lafiya da yan Nigeria suke futa kasashen duniya shima yana daya daga cikin matsalar da yake sanyawa dollars take qara hauhawa, domin kasashe irin su England, America, Germany, India, Egypt, da sauran su, duk yan Nigeria da dollar suke biya gurin neman lafiya.
Kamfanoni duk sun durqushe, dalilan hakan ya zamanto Nigeria bata futar da kayyayaki kasashen duniya balle har ta samo dollar da zasu shigo Nigeria.
Wannan shine dalilin hauhawan dollars, domin buqatun dollars yayi yawa a Nigeria, asa'ilin da samun ta yayi qaranci ga yan Nigeria 🇳🇬.
Mene mafuta? Mafuta muddin ana son samun sauqin hauhawan dollars, shine gwamnatin Nigeria tayi kokarin tada matatan man fetir inda Nigeria zata daina siyan tatacce daga waje, sannan ayi kokarin farfado da kamfanonin da suka durkushe ta yadda Nigeria zata dunga siyar da kaya a kasashen ketare ana biyan ta da dollar, sannan agyara fannin ilimi da lafiya ta yadda yan Nigeria zasu rage futa kasashen waje domin neman su.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
SAKON SARKIN KANO ZUWA GA SHUGABAN KASAN NIGERIA
SAKON SARKIN KANO GA SHUGABAN KASA Yau litinin 12/2/2024 Mai martaba sarkin kano Alh Aminu Ado Bayero CFR CNOL JP ya karbi bakuncin matar sh...
-
SAKON SARKIN KANO GA SHUGABAN KASA Yau litinin 12/2/2024 Mai martaba sarkin kano Alh Aminu Ado Bayero CFR CNOL JP ya karbi bakuncin matar sh...
-
Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi kakkausar suka kan matakin da gwamnatocin Kasashen Yamma suka ɗauka a kan hare-haren da I...
-
Ɓarnar da hare-haren Isra'ila suka yi cikin dare Waɗannan hotunan na nuna irin ɓarnar da luguden wutar Isra'ila ya yi a Birnin Gaza ...
No comments:
Post a Comment