Saturday, October 28, 2023

Amurka Bazata sauya matsayanta akan yancin israila da palasdinuba

Shugaba Joe Biden ya ce Amurka ba za ta canza matsayin da aka san ta a kai ba, game da Isra'ila da al'ummar Falasdinawa, tun kafin 6 ga watan Oktoba, ranar da Hamas ta kai hari cikin Isra'ila. Yayin da yake jawabi a taron manema labarai a gefen Firaministan Australia Anthony Albanese, Biden ya ce dole Isr'ila ''ta yi duk abin da za ta iya yi domin kare fararen hula''. Shugaba Biden ya ce ya kaɗu da jin rahotonnin yadda wasu da ya kira ''Yan kama-wuri-zauna masu tsattsauran ra'ayi'' ke far wa Falasɗinawa a Gabar Yamma da Kogin Jordan. "Suna kai hare-hare kan Falasɗinawa a wuraren da suke da 'yancin zama. Ya kamata a dakatar da wannan", in ji Biden. Ya kara da cewa Amurka na goyon bayan Isra'ila wajen kare kanta daga hare-haren Hamas, kuma "za ta tabbatar Isra'ila ta samu abin da take buƙata don kare kanta daga waɗannan 'yan ta'adda. Wanna tabbas ne." Mista Biden ya ce Hamas ba ta wakiltar "mafi yawan Falasɗinawan Zirin Gaza ko ma a wani wuri da suke". Ya ci gaba da cewa "Hamas ba za ta ci gaba da fakewa a bayan Falasɗinawa fararen hula tana kai wa Isra'ila hare-hare ba".

No comments:

Post a Comment

SAKON SARKIN KANO ZUWA GA SHUGABAN KASAN NIGERIA

SAKON SARKIN KANO GA SHUGABAN KASA Yau litinin 12/2/2024 Mai martaba sarkin kano Alh Aminu Ado Bayero CFR CNOL JP ya karbi bakuncin matar sh...