Tuesday, October 31, 2023

MASU ADAWA AKAN KASHE MATA DA YARA DA ISRAILA TAKEYI A GAZA SUNKATSE BLINKEN YANA TSAKA DA MAGANA AMAJALISAN DATTIJAN AMERICA

Masu zanga-zanga da ke kiran a tsagaita wuta a Gaza sun katse Sakataren Harkokin Wajen Amurka Anthony Blinken a lokacin wani zaman sauraron jin bahasi na Majalisar Dattijai ranar Talata.

Mutane da yawa sun yi cincirindo suna ta kuwwar "A tsagaita wuta yanzu!"

Sakatare Blinken da Sakataren Tsaron Amurka Lloyd Austin na gabatar da jawabi ne game da bukatar fadar White House ta neman amincewa da kudin tsaro dala biliyan 106.

Kudin ya kunshi dala biliyan 14.3 don tallafawa kokarin sojojin Isra'ila a kan kungiyar Hamas.

Suna tsaye daya bayan daya, masu zanga-zangar sun jira har lokacin da Mista Blinken ya fara bayar da bahasi kafin su fara yi masa ihu. Anthony Blinken dai ya dakata yayin da 'yan majalisar ala tilas suka jingine zaman a lokuta da dama.

'Yan sandan da ke kula da ginin majalisar dokokin sun yi hanzari suka rako masu zanga-zangar daga zauren a lokacin da suka fara ihu.

'Yan sanda sun ce an kama mutum 12 saboda yin zanga-zanga ba bisa ka'ida ba a cikin wani sashe na majalisar.

Wasu daga cikin wadanda suka katse zaman majalisar na da alaka da wata kungiya mai adawa da yaki wadda ake kira CODEPINK, ta kuma yi kira ga Amurka ta daina tura makamai Ukraine.

Masu zanga-zangar da dama sun daura kyalle mai rubutu "Ba mu yarda da yi wa Gaza kofar rago ba", daidai lokacin da suke kira ga Amurka ta dakatar da tura wa Isra'ila kudade.

Kungiyar CODEPINK ta tabbatar da cewa an kama wasu daga cikin wakilanta.

Ta ce wasu sun sanya jan fenti a hannuwansu "don nuna alamar jini". Mista Blinken ya yi nuni da masu zanga-zangar a karshen sanarwarsa da cewa, ga kuma "jijiyoyin wuyan da aka tayar a wannan daki".

"Dukkanmu mun dukufa wajen kare fararen hula. Dukkanmu mun san irin wahalhalun da ake ciki a daidai wannan lokaci da muke magana, dukkanmu mun dukufa wajen ganin karshen haka," a cewarsa.

Sai dai ya kara da cewa, abu ne mai muhimmanci ga Amurka ta mara baya ga abokan kawancenta.

Monday, October 30, 2023

LOKACI YAYI DAYA KAMATA ATIKU ABUBAKAR DAN TAKARAR JAM’IYAR ADAWA DAYAKOMA GEFE

Fadar shugaban ƙasar Najeriya ta mayar wa da jagoran adawa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, martani tana mai ba shi shawarar ya "kawo ƙarshen" burinsa na zama shugaban ƙasa.

Martanin na zuwa ne bayan wani taron manema labarai da ya gudanar a yau Litinin, inda ya yi watsi da hukuncin kotun ƙolin da ya jaddada nasarar Shugaba Bola Tinubu na jam'iyyar APC a zaɓen 2023.

Kazalika, Atiku ya ba da shawarar sauya wa'adin mulki zuwa karo ɗaya kuma na shekara shida, da kuma mayar da zaɓe da tattara sakamako ta hanyar latironi su zama tilas a Najeriya.

"....[Atiku] ya mayar da kansa ɗan jagaliya ta hanyar ƙasƙantar da hukumomin ƙasa baki ɗaya don cimma abin da ba zai iya samu ba a akwatin zaɓe," a cewar martanin da Bayo Onanuga - mai taimaka wa shugaban ƙasa kan kafofin yaɗa labarai - ya wallafa a dandalin X.

Ya ƙara da cewa "muna so mu bai wa Atiku shawarar cewa dole ne yanzu ya katse burinsa kuma ya matsa gefe".

Sunday, October 29, 2023

ANHANA MANYAN MOTOCI SHIGA RIGASA

RIGASA

SANARWA  SANARWA SANARWA

Duba da abubuwanda suke gudana da irin barazanarda AL ummar Rigasa ke fuskanta
GA Masu manyan motochi ta Hanyar shigo
Da fetir ko gas ko empty din Mota Wanda suke
Fakin bakin titi da chikin unguwanni. BA bisa
Kaida ba  Wanda Hakan. Ka Iya haifar da gobara  da Hadarin ababen hawa. Da kuka lalata titi

Bisa tattaunawa da Shuwagabanin Qungiyoyin
Direbobi, da Shugabanchin karamar hukumar Igabi, da Hadin guwar masarauta, da hukumar Yan Sanda  da Road safety D kastelia.

AN HARAMTA SHIGOWAR DUK WATA BABBAR
MOTAR MAI KO TA KAYA CHIKIN RIGASA

Sai dai Wacce zata sauke man fetir ko gas a
Gidan man  eyoun ko mobile  ko kamo. Trailer
Kuma  matuqar ba kayan Yan kasuwar Mu na
Rigasa zasu kawo ba suma An Hana,  Amma motar itache Wacce ta dauko itache  zasu Iya
Shigowa  

Akwai  hukumar da aka tanada wayanda zasu
Chigaba da gudanar da Aikin kulawa Don ganin
An gabatar da Wannan doka bisa tsari

Zaa sauke karfen da aka Sanya a Abuja road
Duk Direban da yazo zayyi slow a binchika
Sannan abude masa in Wanda doka ta aminchene ya Shiga

Duk Wanda ya taho da gudu ya karyar karfen
To zaa kama motar har sai an tabbatar da
Ya Gyara dukkan Barnar da yayi

Dafatan zaa kiyaye doka a zauna lafiya Allah ya tsaremu da tsarewarsa amin

Saturday, October 28, 2023

Nigerian Army Announces Recruitment into NDA

The Army on Saturday announced that interested Nigerians can start applying for admission into the Nigerian Defence Academy.

This was revealed on their official X handle. 

The caption reads: 

"APPLICATION FOR ADMISSION INTO THE NIGERIAN DEFENCE ACADEMY 76 REGULAR COURSE. Download PDF here: bitly.ws/YI7C Download Requirements PDF: bitly.ws/YI7V

" Please Beware of Scammers: Always refer to the NDA Website: nda.edu.ng to validate your information."

Gomnati Bazata Tsoma Baki Akan Zabuka Da Za'ayi cikin wota Mai kamawa

Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya ce gwamnatin ƙasar ba za ta yi katsalandan a zaɓukan jihohin Bayelsa da Kogi da kuma Imo ba, da ke tafe cikin watan Nuwamba.

Ribadu, ya bayyana hakan ne ranar Juma'a a lokacin wani taro da shugaban hukumar zaɓen ƙasar, Farfesa Mahmood Yakubu, tare da sauran kwamishinonin zaɓen da sauran masu ruwa da tsaki a sabgar zaɓen.

Ya ce shugaban ƙasar Bola Tinubu na cike da fatan gudanar da sahihin zaɓe a waɗannan jihohi.

“Wannan zaɓuka za su kasance mafiya tsafta fiye da na baya. za su gudana ba tare da rigima ba, za su kasance sahihan zaɓukan da babu katsalandan a cikinsu,” in ji Ribadu.

Ya kuma ce shugaban ƙasa a shirye yake ya goyi bayan hukumar don samun nasarar hakan.

An gudanar da taron ne a ofishinsa a wani ɓangare na tuntuɓa da hukumar ke yi gabanin zaɓukan da ke tafe ranar 11 ga watan Nuwamba.

Tun da farko INEC ta nuna fargabar tsaro gabanin zaɓukan, a wani taro da ta gudanar da jam'iyyun siyasa.

A nasa ɓangare shugaban INEC, ya bayyana fargabarsa kan tsaron lafiyar masu kaɗa ƙuri'a da tsaron kayayyakin zaɓe masu muhimmanci, tare da tsaron cibiyoyin tattara sakamakon zaɓe.

Ya yi kira ga jami'an tsaro su yi maganin duk wanda ya yi yunƙurin tayar da zaune-tsaye a ranar zaɓen.

Birnin Gaza ya Hautsine


Ɓarnar da hare-haren Isra'ila suka yi cikin dare

Waɗannan hotunan na nuna irin ɓarnar da luguden wutar Isra'ila ya yi a Birnin Gaza a tsakar daren da ya gabata.

A jiya Juma'a rundunar sojin ta ce za ta tsananta hare-haren, inda a yau ta tabbatar cewa ta kai hari ta ƙasa kuma har yanzu dakarunta na cikin garin a arewacin Gaza.

SABODA JININ MUSULMAI AKE ZUBARWA SHIYA KASACEN YAMMA SUKAYI WATSI DA DOKA(ERDOGAN)

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi kakkausar suka kan matakin da gwamnatocin Kasashen Yamma suka ɗauka a kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza,

Mista Erdogan ya ce Kasashen Yamma sun kasa ɗaukar matakan da suka dace don magance rikicin saboda jinin Musulmai ake zubarwa.

Shugaban na Turkiya ya nuna shakku kan yadda ake aiwatar da yarjejeniyar kare hakkin dan'adam ta duniya, yana mai cewa da alama ƙasashen yammacin duniya sukan yi watsi da ita, idan ba ta dace da muradunsu ba, musamman idan ya shafi asarar rayukan Musulmai.

A wani muhimmin mataki, Erdogan ya soke ziyarar da ya shirya kai wa Isra'ila tare da nuna nadamar yin musabaha da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a taron Majalisar Dinkin Duniya da aka yi a birnin New York cikin watan jiya.

Wannan yana nuna gagarumin sauyi a dangantakar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.

A halin da ake ciki kuma, ministan harkokin wajen gwamnatin Falasɗinawa, Riyad al-Maliki, da ke kula da Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, ba Gaza ba, ya bayyana hare-haren da Isra'ila ta kai a matsayin "yakin ɗaukar fansa."

Da yake jawabi a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da ke kasar Netherlands, al-Maliki ya jaddada cewa harin bama-bamai a Gaza na baya-bayan nan ya fi tsanani fiye da hare-haren da Isra'ila ta kai a baya.

Ya kuma yi kira a gaggauta tsagaita wuta.

SAKON SARKIN KANO ZUWA GA SHUGABAN KASAN NIGERIA

SAKON SARKIN KANO GA SHUGABAN KASA Yau litinin 12/2/2024 Mai martaba sarkin kano Alh Aminu Ado Bayero CFR CNOL JP ya karbi bakuncin matar sh...