Tuesday, October 31, 2023

MASU ADAWA AKAN KASHE MATA DA YARA DA ISRAILA TAKEYI A GAZA SUNKATSE BLINKEN YANA TSAKA DA MAGANA AMAJALISAN DATTIJAN AMERICA

Masu zanga-zanga da ke kiran a tsagaita wuta a Gaza sun katse Sakataren Harkokin Wajen Amurka Anthony Blinken a lokacin wani zaman sauraron jin bahasi na Majalisar Dattijai ranar Talata.

Mutane da yawa sun yi cincirindo suna ta kuwwar "A tsagaita wuta yanzu!"

Sakatare Blinken da Sakataren Tsaron Amurka Lloyd Austin na gabatar da jawabi ne game da bukatar fadar White House ta neman amincewa da kudin tsaro dala biliyan 106.

Kudin ya kunshi dala biliyan 14.3 don tallafawa kokarin sojojin Isra'ila a kan kungiyar Hamas.

Suna tsaye daya bayan daya, masu zanga-zangar sun jira har lokacin da Mista Blinken ya fara bayar da bahasi kafin su fara yi masa ihu. Anthony Blinken dai ya dakata yayin da 'yan majalisar ala tilas suka jingine zaman a lokuta da dama.

'Yan sandan da ke kula da ginin majalisar dokokin sun yi hanzari suka rako masu zanga-zangar daga zauren a lokacin da suka fara ihu.

'Yan sanda sun ce an kama mutum 12 saboda yin zanga-zanga ba bisa ka'ida ba a cikin wani sashe na majalisar.

Wasu daga cikin wadanda suka katse zaman majalisar na da alaka da wata kungiya mai adawa da yaki wadda ake kira CODEPINK, ta kuma yi kira ga Amurka ta daina tura makamai Ukraine.

Masu zanga-zangar da dama sun daura kyalle mai rubutu "Ba mu yarda da yi wa Gaza kofar rago ba", daidai lokacin da suke kira ga Amurka ta dakatar da tura wa Isra'ila kudade.

Kungiyar CODEPINK ta tabbatar da cewa an kama wasu daga cikin wakilanta.

Ta ce wasu sun sanya jan fenti a hannuwansu "don nuna alamar jini". Mista Blinken ya yi nuni da masu zanga-zangar a karshen sanarwarsa da cewa, ga kuma "jijiyoyin wuyan da aka tayar a wannan daki".

"Dukkanmu mun dukufa wajen kare fararen hula. Dukkanmu mun san irin wahalhalun da ake ciki a daidai wannan lokaci da muke magana, dukkanmu mun dukufa wajen ganin karshen haka," a cewarsa.

Sai dai ya kara da cewa, abu ne mai muhimmanci ga Amurka ta mara baya ga abokan kawancenta.

No comments:

Post a Comment

SAKON SARKIN KANO ZUWA GA SHUGABAN KASAN NIGERIA

SAKON SARKIN KANO GA SHUGABAN KASA Yau litinin 12/2/2024 Mai martaba sarkin kano Alh Aminu Ado Bayero CFR CNOL JP ya karbi bakuncin matar sh...