A daren da ya gabata Isra'ila ta tsananta luguden wuta kan yankin Gaza fiye da sauran darare a baya, lamarin da ya sanya aka gaza sadarwa da al'ummar yankin, abin da ke nuna cewa da alama hanyoyin sadarwa sun katse.
Isra'ila a ɓangare ɗaya ta tabbatar da cewa dakarunta na ƙara faɗaɗa samamen da suke yi ta ƙasa.
Cibiyar da ke sanya ido kan harkokin intanet mai suna Netblocks ta wallafa a shafinta na X cewa "an samu katsewar intanet."
Kungiyar bayar da agaji ta Red Crescent da ke aiki a yankin ta ce ta kasa yin magana da jami'anta da ke cikin Gaza.
Kungiyar ta rubuta a shafinta na X cewa "Akwai damuwa game da ko tawagarmu za ta iya ci gaba da aikinta na bayar da agajin kiwon lafiya, musamman ganin cewa wannan katsewar sadarwa ta shafi lambar neman agajin gaggawa ta 101."
A jiya Juma'a ne dakarun Isra'ila suka sake umurtar Falasɗinawa su ƙara matsawa zuwa kudancin yankin Gaza bayan sanar da cewa za su faɗaɗa ayyukansu na soji.
A lokacin wata sanarwa ga manema labaru, mai magana da yawun rundunar sojin Isra'ila, Daniel Hagari ya ce sojoji sun "tsananta hare-hare kan Gaza. Sojojin sama suka kai farmaki ne kan maɓuya na ƙarƙashin ƙasa da kuma cibiyoyin ƴan ta'adda."
"A ci gaba da ayyukan da muka fara a ƴan kwanakin da suka gabata, dakarun ƙasa za su faɗaɗa hare-harensu a wannan yammaci."
Yanzu haka dai hanyar sadarwa ta katse tsakanin mutanen Gaza da sauran duniya, don haka akwai ƙarancin bayanai kan halin da ake ciki.
BBC ta yi ƙoƙarin tura saƙo ta manhajar Whatsapp zuwa Gazar, kuma tun daga yamma da aka tura shi har yanzu yana nuna bai sauka a wayar da aka tura ba.
Haka nan kuma, kiran waya ba ya shiga duk wani layin waya da ke Gazar.
BBC ta yi yunƙurin kiran lambobin waya da dama, amma duk ba su shiga ba.
Kamfanin sadarwa na Jawwal da ke aiki a yankin Falasɗinawa ya ce an yanke duk wata hanyar sadarwa a zirin Gaza.
BBC ta kuma nemi jin bayani daga rundunar sojin Isra’ila game da wannan batu, amma har yanzu babu wanda ya yi wani bayani a kai.
Allah yadaukaka musulunci DA musulmai yakawo zaman lpia a Gaza
ReplyDelete