Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi kakkausar suka kan matakin da gwamnatocin Kasashen Yamma suka ɗauka a kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza,
Mista Erdogan ya ce Kasashen Yamma sun kasa ɗaukar matakan da suka dace don magance rikicin saboda jinin Musulmai ake zubarwa.
Shugaban na Turkiya ya nuna shakku kan yadda ake aiwatar da yarjejeniyar kare hakkin dan'adam ta duniya, yana mai cewa da alama ƙasashen yammacin duniya sukan yi watsi da ita, idan ba ta dace da muradunsu ba, musamman idan ya shafi asarar rayukan Musulmai.
A wani muhimmin mataki, Erdogan ya soke ziyarar da ya shirya kai wa Isra'ila tare da nuna nadamar yin musabaha da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a taron Majalisar Dinkin Duniya da aka yi a birnin New York cikin watan jiya.
Wannan yana nuna gagarumin sauyi a dangantakar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.
A halin da ake ciki kuma, ministan harkokin wajen gwamnatin Falasɗinawa, Riyad al-Maliki, da ke kula da Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, ba Gaza ba, ya bayyana hare-haren da Isra'ila ta kai a matsayin "yakin ɗaukar fansa."
Da yake jawabi a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da ke kasar Netherlands, al-Maliki ya jaddada cewa harin bama-bamai a Gaza na baya-bayan nan ya fi tsanani fiye da hare-haren da Isra'ila ta kai a baya.
Ya kuma yi kira a gaggauta tsagaita wuta.