SAKON SARKIN KANO GA SHUGABAN KASA
Yau litinin 12/2/2024 Mai martaba sarkin kano Alh Aminu Ado Bayero CFR CNOL JP ya karbi bakuncin matar shugaban kasar Nigeria Senator Oluremi Tinubu a fadarsa ta soron ENGLAND. Ga kadan daga cikin jawabin Mai martaba sarkin kano
1 - Mai martaba sarki ya shaidawa matar shugaban kasa cewa ta shaidawa shugaban kasar cewa ya kamata a duba yanayin da jama'ar Nigeria suke ciki na kuncin rayuwa da kuma tsadar kayan Abinci
2 - Mai martaba sarkin ya kuma shaidawa matar shugaban kasar cewa, Akullun yana samun korafe-korafe na jama'a akan cewa ammeyar da wani yanki na CBN da FAAN da kuma wasu manyan ma'aikatu jahar legas ya kamata shima ta sanarwa da shugaban kasar cewa aduba wannan maganar saboda masalahar jama'a
3 - Mai martaba sarkin kano ya kuma shaidawa matar shugaban kasar cewa ya kamata aduba yanayin tsaron da arewacin Nigeria ke ciki saboda tausayawa Al'umma, shima yace ta shaidawa shugaban kasar wannan korafi
4 - Mai martaba sarkin kano ya kuma shaidawa matar shugaban kasar cewa, ya kamata indai zasuyi ayuka na Alkhairi su dinga duba jahar kano saboda mumfi kowa yawan Al'umma a Nigeria saboda lokacin da akayi kidayar jama'a mune na daya a Nigeria. Yace shima ta shaidawa shugaban kasar wannan muhimmin sako da ya fadaa
Matar shugaban kasar tana tare da yan rakiyarta, Kamar Gwamnan jahar Benue da mataimakin shugaban majalisar Dattawan Nigeria Hon Barau I Jibrin da karamar ministan Abuja Dr Mariya Bunkure da matar Gwamnan jahar kano da matar shugaban DSS na kasa da kwamishinan yan sanda na jahar kano CP Muhammad Husaini Gumel da kuma manyan jami'an Gwamnatin tarayyar Nigeria dana kano