NITDA 3MTT Program: BAYANI GA MASU CIKAWA DA ABINDA YAKAMATA KACIKA HADI MA'ANONIN BANGARORI GUDA 12 (RUBUTU MAI TSAYI) KASHI NA DAYA
NITDA ta shirya tsaf domin horar da ƴan kasa akalla miliyan 12 a fannin ilmin fasaha har guda sha biyu. Wadannan ilmum mummuka sune kamar haka:
1. Software development
2. UI/UX design
3. Data Analysis & Visualisation
4. Quality Assurance
5. Product Management
6. Data Science
7. Animation
8. AI / ML
9. Cybersecurity
10. Game development
11. Cloud Computing
12. Dev Ops
Bangarorin nan guda 12 sune wanda NITDA ta kudiri aniyar horarda ƴan kasa karkashinta saboda asamu damar rage radadin rashin aikin yi sakanin al'umma. Lallai yana da kyau mutanen mu in da su cika sosai domin samun gurbin karatun a bangaren horarwan sai dai, kafinnan yanada matukar kyau a fahimci amfanin kowane bangarorin ko kuma ma'anoninsu kafin mutum yacika. Sai dai ba sai wanda yake da ilmin “Computer Cikakkiya” bane kadai zai cika inma daga Sociology kake akwai inda yakamata. Bini a sannu INSHA ALLAH zanyi cikakkiyar bayani kowane bangare da abinda ke cikin sa, sai dai rubutun zai iya yuwa yayi tsayi sosai dan haka sai anyi hakuri wajen karantawa.
Wannan “Shirin” an rabashi biyu akwai “Training Providers” da kuma “Trainee”.
Training Providers zaka cikashi ne idan kanaso kazamto cikin wadanda zasu gabatar da horarwar da ga daliban wato “Trainee”. Idan kana da kwarewa a kowane bangare acikin wadannan bangarori sha biyun zaka iya neman gurbin horarwar ta hanyar Applying a shafinsu na NITDA.
Ko kuma aje: https://3mtt.nitda.gov.ng/
Sannan a sauke Brochure na Training Providers domin samun cikakken bayani amma kafinnan ga takaitaccen bayani ga duk wanda keson shiga matsayin Training Provider.
Ana bukatar mutum yacika wadannan ka'idojin
1. Organization din mutum yazamto yana rajista da gwamnati ma'ana yazamto registered company a karkashin CAC.
2. Yazamto yana da kwararrun ma'aikata da suke da kwarewa wajen horarwa.
3. Yazamto yana da dukkan kayayyaki da ake bukata wajen horarwar.
4. Yazamto zai iya samarwa akalla kashi 50% na daliban da ya horar aiki cikin watanni uku da kammala horarwar.
Wadannan sune ka'idojin a dunkule da ake bukata a wajen dukkan wani ko wasu suke son shiga matsayin Training Providers.
Wannan na nufin mutum shi kadai bazaiyu yashiga a matsayin “Training Provider” ba sai idan yanada wani kamfani ko kuma yana da wani alaqa da wani kamfanin.
No comments:
Post a Comment