Tuesday, October 31, 2023

MASU ADAWA AKAN KASHE MATA DA YARA DA ISRAILA TAKEYI A GAZA SUNKATSE BLINKEN YANA TSAKA DA MAGANA AMAJALISAN DATTIJAN AMERICA

Masu zanga-zanga da ke kiran a tsagaita wuta a Gaza sun katse Sakataren Harkokin Wajen Amurka Anthony Blinken a lokacin wani zaman sauraron jin bahasi na Majalisar Dattijai ranar Talata.

Mutane da yawa sun yi cincirindo suna ta kuwwar "A tsagaita wuta yanzu!"

Sakatare Blinken da Sakataren Tsaron Amurka Lloyd Austin na gabatar da jawabi ne game da bukatar fadar White House ta neman amincewa da kudin tsaro dala biliyan 106.

Kudin ya kunshi dala biliyan 14.3 don tallafawa kokarin sojojin Isra'ila a kan kungiyar Hamas.

Suna tsaye daya bayan daya, masu zanga-zangar sun jira har lokacin da Mista Blinken ya fara bayar da bahasi kafin su fara yi masa ihu. Anthony Blinken dai ya dakata yayin da 'yan majalisar ala tilas suka jingine zaman a lokuta da dama.

'Yan sandan da ke kula da ginin majalisar dokokin sun yi hanzari suka rako masu zanga-zangar daga zauren a lokacin da suka fara ihu.

'Yan sanda sun ce an kama mutum 12 saboda yin zanga-zanga ba bisa ka'ida ba a cikin wani sashe na majalisar.

Wasu daga cikin wadanda suka katse zaman majalisar na da alaka da wata kungiya mai adawa da yaki wadda ake kira CODEPINK, ta kuma yi kira ga Amurka ta daina tura makamai Ukraine.

Masu zanga-zangar da dama sun daura kyalle mai rubutu "Ba mu yarda da yi wa Gaza kofar rago ba", daidai lokacin da suke kira ga Amurka ta dakatar da tura wa Isra'ila kudade.

Kungiyar CODEPINK ta tabbatar da cewa an kama wasu daga cikin wakilanta.

Ta ce wasu sun sanya jan fenti a hannuwansu "don nuna alamar jini". Mista Blinken ya yi nuni da masu zanga-zangar a karshen sanarwarsa da cewa, ga kuma "jijiyoyin wuyan da aka tayar a wannan daki".

"Dukkanmu mun dukufa wajen kare fararen hula. Dukkanmu mun san irin wahalhalun da ake ciki a daidai wannan lokaci da muke magana, dukkanmu mun dukufa wajen ganin karshen haka," a cewarsa.

Sai dai ya kara da cewa, abu ne mai muhimmanci ga Amurka ta mara baya ga abokan kawancenta.

Monday, October 30, 2023

LOKACI YAYI DAYA KAMATA ATIKU ABUBAKAR DAN TAKARAR JAM’IYAR ADAWA DAYAKOMA GEFE

Fadar shugaban ƙasar Najeriya ta mayar wa da jagoran adawa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, martani tana mai ba shi shawarar ya "kawo ƙarshen" burinsa na zama shugaban ƙasa.

Martanin na zuwa ne bayan wani taron manema labarai da ya gudanar a yau Litinin, inda ya yi watsi da hukuncin kotun ƙolin da ya jaddada nasarar Shugaba Bola Tinubu na jam'iyyar APC a zaɓen 2023.

Kazalika, Atiku ya ba da shawarar sauya wa'adin mulki zuwa karo ɗaya kuma na shekara shida, da kuma mayar da zaɓe da tattara sakamako ta hanyar latironi su zama tilas a Najeriya.

"....[Atiku] ya mayar da kansa ɗan jagaliya ta hanyar ƙasƙantar da hukumomin ƙasa baki ɗaya don cimma abin da ba zai iya samu ba a akwatin zaɓe," a cewar martanin da Bayo Onanuga - mai taimaka wa shugaban ƙasa kan kafofin yaɗa labarai - ya wallafa a dandalin X.

Ya ƙara da cewa "muna so mu bai wa Atiku shawarar cewa dole ne yanzu ya katse burinsa kuma ya matsa gefe".

Sunday, October 29, 2023

ANHANA MANYAN MOTOCI SHIGA RIGASA

RIGASA

SANARWA  SANARWA SANARWA

Duba da abubuwanda suke gudana da irin barazanarda AL ummar Rigasa ke fuskanta
GA Masu manyan motochi ta Hanyar shigo
Da fetir ko gas ko empty din Mota Wanda suke
Fakin bakin titi da chikin unguwanni. BA bisa
Kaida ba  Wanda Hakan. Ka Iya haifar da gobara  da Hadarin ababen hawa. Da kuka lalata titi

Bisa tattaunawa da Shuwagabanin Qungiyoyin
Direbobi, da Shugabanchin karamar hukumar Igabi, da Hadin guwar masarauta, da hukumar Yan Sanda  da Road safety D kastelia.

AN HARAMTA SHIGOWAR DUK WATA BABBAR
MOTAR MAI KO TA KAYA CHIKIN RIGASA

Sai dai Wacce zata sauke man fetir ko gas a
Gidan man  eyoun ko mobile  ko kamo. Trailer
Kuma  matuqar ba kayan Yan kasuwar Mu na
Rigasa zasu kawo ba suma An Hana,  Amma motar itache Wacce ta dauko itache  zasu Iya
Shigowa  

Akwai  hukumar da aka tanada wayanda zasu
Chigaba da gudanar da Aikin kulawa Don ganin
An gabatar da Wannan doka bisa tsari

Zaa sauke karfen da aka Sanya a Abuja road
Duk Direban da yazo zayyi slow a binchika
Sannan abude masa in Wanda doka ta aminchene ya Shiga

Duk Wanda ya taho da gudu ya karyar karfen
To zaa kama motar har sai an tabbatar da
Ya Gyara dukkan Barnar da yayi

Dafatan zaa kiyaye doka a zauna lafiya Allah ya tsaremu da tsarewarsa amin

Saturday, October 28, 2023

Nigerian Army Announces Recruitment into NDA

The Army on Saturday announced that interested Nigerians can start applying for admission into the Nigerian Defence Academy.

This was revealed on their official X handle. 

The caption reads: 

"APPLICATION FOR ADMISSION INTO THE NIGERIAN DEFENCE ACADEMY 76 REGULAR COURSE. Download PDF here: bitly.ws/YI7C Download Requirements PDF: bitly.ws/YI7V

" Please Beware of Scammers: Always refer to the NDA Website: nda.edu.ng to validate your information."

Gomnati Bazata Tsoma Baki Akan Zabuka Da Za'ayi cikin wota Mai kamawa

Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya ce gwamnatin ƙasar ba za ta yi katsalandan a zaɓukan jihohin Bayelsa da Kogi da kuma Imo ba, da ke tafe cikin watan Nuwamba.

Ribadu, ya bayyana hakan ne ranar Juma'a a lokacin wani taro da shugaban hukumar zaɓen ƙasar, Farfesa Mahmood Yakubu, tare da sauran kwamishinonin zaɓen da sauran masu ruwa da tsaki a sabgar zaɓen.

Ya ce shugaban ƙasar Bola Tinubu na cike da fatan gudanar da sahihin zaɓe a waɗannan jihohi.

“Wannan zaɓuka za su kasance mafiya tsafta fiye da na baya. za su gudana ba tare da rigima ba, za su kasance sahihan zaɓukan da babu katsalandan a cikinsu,” in ji Ribadu.

Ya kuma ce shugaban ƙasa a shirye yake ya goyi bayan hukumar don samun nasarar hakan.

An gudanar da taron ne a ofishinsa a wani ɓangare na tuntuɓa da hukumar ke yi gabanin zaɓukan da ke tafe ranar 11 ga watan Nuwamba.

Tun da farko INEC ta nuna fargabar tsaro gabanin zaɓukan, a wani taro da ta gudanar da jam'iyyun siyasa.

A nasa ɓangare shugaban INEC, ya bayyana fargabarsa kan tsaron lafiyar masu kaɗa ƙuri'a da tsaron kayayyakin zaɓe masu muhimmanci, tare da tsaron cibiyoyin tattara sakamakon zaɓe.

Ya yi kira ga jami'an tsaro su yi maganin duk wanda ya yi yunƙurin tayar da zaune-tsaye a ranar zaɓen.

Birnin Gaza ya Hautsine


Ɓarnar da hare-haren Isra'ila suka yi cikin dare

Waɗannan hotunan na nuna irin ɓarnar da luguden wutar Isra'ila ya yi a Birnin Gaza a tsakar daren da ya gabata.

A jiya Juma'a rundunar sojin ta ce za ta tsananta hare-haren, inda a yau ta tabbatar cewa ta kai hari ta ƙasa kuma har yanzu dakarunta na cikin garin a arewacin Gaza.

SABODA JININ MUSULMAI AKE ZUBARWA SHIYA KASACEN YAMMA SUKAYI WATSI DA DOKA(ERDOGAN)

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi kakkausar suka kan matakin da gwamnatocin Kasashen Yamma suka ɗauka a kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza,

Mista Erdogan ya ce Kasashen Yamma sun kasa ɗaukar matakan da suka dace don magance rikicin saboda jinin Musulmai ake zubarwa.

Shugaban na Turkiya ya nuna shakku kan yadda ake aiwatar da yarjejeniyar kare hakkin dan'adam ta duniya, yana mai cewa da alama ƙasashen yammacin duniya sukan yi watsi da ita, idan ba ta dace da muradunsu ba, musamman idan ya shafi asarar rayukan Musulmai.

A wani muhimmin mataki, Erdogan ya soke ziyarar da ya shirya kai wa Isra'ila tare da nuna nadamar yin musabaha da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a taron Majalisar Dinkin Duniya da aka yi a birnin New York cikin watan jiya.

Wannan yana nuna gagarumin sauyi a dangantakar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.

A halin da ake ciki kuma, ministan harkokin wajen gwamnatin Falasɗinawa, Riyad al-Maliki, da ke kula da Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, ba Gaza ba, ya bayyana hare-haren da Isra'ila ta kai a matsayin "yakin ɗaukar fansa."

Da yake jawabi a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da ke kasar Netherlands, al-Maliki ya jaddada cewa harin bama-bamai a Gaza na baya-bayan nan ya fi tsanani fiye da hare-haren da Isra'ila ta kai a baya.

Ya kuma yi kira a gaggauta tsagaita wuta.

IPhone 13 pro max

Hanyoyin Sadarwa Sun Katse a Gaza


A daren da ya gabata Isra'ila ta tsananta luguden wuta kan yankin Gaza fiye da sauran darare a baya, lamarin da ya sanya aka gaza sadarwa da al'ummar yankin, abin da ke nuna cewa da alama hanyoyin sadarwa sun katse.

Isra'ila a ɓangare ɗaya ta tabbatar da cewa dakarunta na ƙara faɗaɗa samamen da suke yi ta ƙasa.

Cibiyar da ke sanya ido kan harkokin intanet mai suna Netblocks ta wallafa a shafinta na X cewa "an samu katsewar intanet."

Kungiyar bayar da agaji ta Red Crescent da ke aiki a yankin ta ce ta kasa yin magana da jami'anta da ke cikin Gaza.

Kungiyar ta rubuta a shafinta na X cewa "Akwai damuwa game da ko tawagarmu za ta iya ci gaba da aikinta na bayar da agajin kiwon lafiya, musamman ganin cewa wannan katsewar sadarwa ta shafi lambar neman agajin gaggawa ta 101."

A jiya Juma'a ne dakarun Isra'ila suka sake umurtar Falasɗinawa su ƙara matsawa zuwa kudancin yankin Gaza bayan sanar da cewa za su faɗaɗa ayyukansu na soji.

A lokacin wata sanarwa ga manema labaru, mai magana da yawun rundunar sojin Isra'ila, Daniel Hagari ya ce sojoji sun "tsananta hare-hare kan Gaza. Sojojin sama suka kai farmaki ne kan maɓuya na ƙarƙashin ƙasa da kuma cibiyoyin ƴan ta'adda."

"A ci gaba da ayyukan da muka fara a ƴan kwanakin da suka gabata, dakarun ƙasa za su faɗaɗa hare-harensu a wannan yammaci."

Yanzu haka dai hanyar sadarwa ta katse tsakanin mutanen Gaza da sauran duniya, don haka akwai ƙarancin bayanai kan halin da ake ciki.

BBC ta yi ƙoƙarin tura saƙo ta manhajar Whatsapp zuwa Gazar, kuma tun daga yamma da aka tura shi har yanzu yana nuna bai sauka a wayar da aka tura ba.

Haka nan kuma, kiran waya ba ya shiga duk wani layin waya da ke Gazar.

BBC ta yi yunƙurin kiran lambobin waya da dama, amma duk ba su shiga ba.

Kamfanin sadarwa na Jawwal da ke aiki a yankin Falasɗinawa ya ce an yanke duk wata hanyar sadarwa a zirin Gaza.

BBC ta kuma nemi jin bayani daga rundunar sojin Isra’ila game da wannan batu, amma har yanzu babu wanda ya yi wani bayani a kai.

IPhone 15 pro max

You can visit our store for your affordable price

Amurka Bazata sauya matsayanta akan yancin israila da palasdinuba

Shugaba Joe Biden ya ce Amurka ba za ta canza matsayin da aka san ta a kai ba, game da Isra'ila da al'ummar Falasdinawa, tun kafin 6 ga watan Oktoba, ranar da Hamas ta kai hari cikin Isra'ila. Yayin da yake jawabi a taron manema labarai a gefen Firaministan Australia Anthony Albanese, Biden ya ce dole Isr'ila ''ta yi duk abin da za ta iya yi domin kare fararen hula''. Shugaba Biden ya ce ya kaɗu da jin rahotonnin yadda wasu da ya kira ''Yan kama-wuri-zauna masu tsattsauran ra'ayi'' ke far wa Falasɗinawa a Gabar Yamma da Kogin Jordan. "Suna kai hare-hare kan Falasɗinawa a wuraren da suke da 'yancin zama. Ya kamata a dakatar da wannan", in ji Biden. Ya kara da cewa Amurka na goyon bayan Isra'ila wajen kare kanta daga hare-haren Hamas, kuma "za ta tabbatar Isra'ila ta samu abin da take buƙata don kare kanta daga waɗannan 'yan ta'adda. Wanna tabbas ne." Mista Biden ya ce Hamas ba ta wakiltar "mafi yawan Falasɗinawan Zirin Gaza ko ma a wani wuri da suke". Ya ci gaba da cewa "Hamas ba za ta ci gaba da fakewa a bayan Falasɗinawa fararen hula tana kai wa Isra'ila hare-hare ba".

Friday, October 27, 2023

TASHIN DOLLA DAKUMA FADUWAR NAIRA

Meye yake kawo tashin dollar a Nigeria 🇳🇬? Masani ilimin tattalin arziki sun bayyana cewar, kusan kashi 80% cikin 100% na kayan da Nigeria take amfani dasu kayan kasashen waje kuma da dollar ake siyo su. Kusan danyan man fetir ne kadai Nigeria take futa da shi kasar waje wanda ake biyan ta dollar, sannan kuma itama ta bada maqudan dollars domin abata tatatcen man. Atadalilin tabarbarewa ilimin primary, Secondary, dakuma university a Nigeria, ya zamanto masu kudi da masu riqe da madafun iko a Nigeria 🇳🇬 yayan su a kasashen waje suke karatu, kuma mafi yawan makarantun da suke zuwa a England, America, Dubai dakuma sauran kasashen duniya duk da dollar ake biyan kudaden makarantun. Fanin neman lafiya da yan Nigeria suke futa kasashen duniya shima yana daya daga cikin matsalar da yake sanyawa dollars take qara hauhawa, domin kasashe irin su England, America, Germany, India, Egypt, da sauran su, duk yan Nigeria da dollar suke biya gurin neman lafiya. Kamfanoni duk sun durqushe, dalilan hakan ya zamanto Nigeria bata futar da kayyayaki kasashen duniya balle har ta samo dollar da zasu shigo Nigeria. Wannan shine dalilin hauhawan dollars, domin buqatun dollars yayi yawa a Nigeria, asa'ilin da samun ta yayi qaranci ga yan Nigeria 🇳🇬. Mene mafuta? Mafuta muddin ana son samun sauqin hauhawan dollars, shine gwamnatin Nigeria tayi kokarin tada matatan man fetir inda Nigeria zata daina siyan tatacce daga waje, sannan ayi kokarin farfado da kamfanonin da suka durkushe ta yadda Nigeria zata dunga siyar da kaya a kasashen ketare ana biyan ta da dollar, sannan agyara fannin ilimi da lafiya ta yadda yan Nigeria zasu rage futa kasashen waje domin neman su.

SAKON SARKIN KANO ZUWA GA SHUGABAN KASAN NIGERIA

SAKON SARKIN KANO GA SHUGABAN KASA Yau litinin 12/2/2024 Mai martaba sarkin kano Alh Aminu Ado Bayero CFR CNOL JP ya karbi bakuncin matar sh...