Monday, February 12, 2024

SAKON SARKIN KANO ZUWA GA SHUGABAN KASAN NIGERIA

SAKON SARKIN KANO GA SHUGABAN KASA
Yau litinin 12/2/2024 Mai martaba sarkin kano Alh Aminu Ado Bayero CFR CNOL JP ya karbi bakuncin matar shugaban kasar Nigeria Senator Oluremi Tinubu a fadarsa ta soron ENGLAND. Ga kadan daga cikin jawabin Mai martaba sarkin kano 

1 - Mai martaba sarki ya shaidawa matar shugaban kasa cewa ta shaidawa shugaban kasar cewa ya kamata a duba yanayin da jama'ar Nigeria suke ciki na kuncin rayuwa da kuma tsadar kayan Abinci 

2 - Mai martaba sarkin ya kuma shaidawa matar shugaban kasar cewa, Akullun yana samun korafe-korafe na jama'a akan cewa ammeyar da wani yanki na CBN da FAAN da kuma wasu manyan ma'aikatu jahar legas ya kamata shima ta sanarwa da shugaban kasar cewa aduba wannan maganar saboda masalahar jama'a 

3 - Mai martaba sarkin kano ya kuma shaidawa matar shugaban kasar cewa ya kamata aduba yanayin tsaron da arewacin Nigeria ke ciki saboda tausayawa Al'umma, shima yace ta shaidawa shugaban kasar wannan korafi 

4 - Mai martaba sarkin kano ya kuma shaidawa matar shugaban kasar cewa, ya kamata indai zasuyi ayuka na Alkhairi su dinga duba jahar kano saboda mumfi kowa yawan Al'umma a  Nigeria saboda lokacin da akayi kidayar jama'a mune na daya a Nigeria. Yace shima ta shaidawa shugaban kasar wannan muhimmin sako da ya fadaa

Matar shugaban kasar tana tare da yan rakiyarta, Kamar Gwamnan jahar Benue da mataimakin shugaban majalisar Dattawan Nigeria Hon Barau I Jibrin da karamar ministan Abuja Dr Mariya Bunkure da matar Gwamnan jahar kano da matar shugaban DSS na kasa da kwamishinan yan sanda na jahar kano CP Muhammad Husaini Gumel da kuma manyan jami'an Gwamnatin tarayyar Nigeria dana kano 

Daga karshe Mai martaba sarkin kano ya yiwa mata shugaban kasar Nigeria fatan alkhairi da kuma yanda tazo kano ziyarar aiki lafiya Allah ya maida ita gida lafiya Amin. Ran sarki ya dade

Thursday, November 2, 2023

Samsung GalaxyZ fold3 5G

HUKUMAR NITDA TAPITO DAWONI TSARI NA KOYARDA WOSU ILMUMMUKA ABANGARE DABAN DABAN WONDA ZAI KIRKIROMA YAN NIGERIA SANA'AN DOGARO DA KANSU

NITDA 3MTT Program: BAYANI GA MASU CIKAWA DA ABINDA YAKAMATA KACIKA HADI MA'ANONIN BANGARORI GUDA 12 (RUBUTU MAI TSAYI) KASHI NA DAYA

NITDA ta shirya tsaf domin horar da ƴan kasa akalla miliyan 12 a fannin ilmin fasaha har guda sha biyu. Wadannan ilmum mummuka sune kamar haka:

1. Software development
2. UI/UX design
3. Data Analysis & Visualisation
4. Quality Assurance
5. Product Management
6. Data Science
7. Animation
8. AI / ML
9. Cybersecurity
10. Game development
11. Cloud Computing
12. Dev Ops

Bangarorin nan guda 12 sune wanda NITDA ta kudiri aniyar horarda ƴan kasa karkashinta saboda asamu damar rage radadin rashin aikin yi sakanin al'umma. Lallai yana da kyau mutanen mu in da su cika sosai domin samun gurbin karatun a bangaren horarwan sai dai, kafinnan yanada matukar kyau a fahimci amfanin kowane bangarorin ko kuma ma'anoninsu kafin mutum yacika. Sai dai ba sai wanda yake da ilmin “Computer Cikakkiya” bane kadai zai cika inma daga Sociology kake akwai inda yakamata. Bini a sannu INSHA ALLAH zanyi cikakkiyar bayani kowane bangare da abinda ke cikin sa, sai dai rubutun zai iya yuwa yayi tsayi sosai dan haka sai anyi hakuri wajen karantawa.

Wannan “Shirin” an rabashi biyu akwai “Training Providers” da kuma “Trainee”.
Training Providers zaka cikashi ne idan kanaso kazamto cikin wadanda zasu gabatar da horarwar da ga daliban wato “Trainee”. Idan kana da kwarewa a kowane bangare acikin wadannan bangarori sha biyun zaka iya neman gurbin horarwar ta hanyar Applying a shafinsu na NITDA. 

Ko kuma aje: https://3mtt.nitda.gov.ng/

Sannan a sauke Brochure na Training Providers domin samun cikakken bayani amma kafinnan ga takaitaccen bayani ga duk wanda keson shiga matsayin Training Provider.

Ana bukatar mutum yacika wadannan ka'idojin

1. Organization din mutum yazamto yana rajista da gwamnati ma'ana yazamto registered company a karkashin CAC.

2. Yazamto yana da kwararrun ma'aikata da suke da kwarewa wajen horarwa.

3. Yazamto yana da dukkan kayayyaki da ake bukata wajen horarwar.

4. Yazamto zai iya samarwa akalla kashi 50% na daliban da ya horar aiki cikin watanni uku da kammala horarwar.

Wadannan sune ka'idojin a dunkule da ake bukata a wajen dukkan wani ko wasu suke son shiga matsayin Training Providers. 

Wannan na nufin mutum shi kadai bazaiyu yashiga a matsayin “Training Provider” ba sai idan yanada wani kamfani ko kuma yana da wani alaqa da wani kamfanin.

ANA ZARGIN BOKO HARAM DA KASHE AKALLA MUTUM 40 A JIHAR YOBE

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Yobe ta ce wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun halaka aƙalla mutum 40 a jihar da ke arewa maso gabashin ƙasar tsakanin ranakun Litinin da Talata.

Sun ce mayaƙan sun riƙa harbin mutane da bindiga da kuma jefa masu bam.

Ana ganin cewa wannan shi ne wani hari mafi muni da aka kai a jihar cikin wata 18.

Ƴan sintiri da ke aikin samar da tsaro a yankin sun ce mayaƙan na Boko Haram sun kai musu harin ne bayan da mazauna ƙauyukan suka ƙi biyan kuɗaɗen harajin da ƴan bindigar suka ƙaƙaba musu.

Mai magana da yawun 'yan sandan Yobe ya faɗa wa BBC Hausa cewa maharan sun fara kai hari ne ranar Talata tare da kashe gomman mutane a yankin ƙaramar hukumar Geidem.

'Yan bindigar sun sake far wa masu zaman makoki a ranar Laraba, inda nan ma suka kashe mutane da yawa.

Ya ce har yanzu ba su kai ga tattara alƙaluman waɗanda aka kashe ba, amma mazauna yankin na cewa adadinsu ya kai kusan 40.

Sau da dama gungun ƴan bindiga a wasu ƙauyukan Najeriya kan nemi mazauna yankunan su biya haraji a wani yunƙuri na tabbatar da ikonsu.

Tuesday, October 31, 2023

MASU ADAWA AKAN KASHE MATA DA YARA DA ISRAILA TAKEYI A GAZA SUNKATSE BLINKEN YANA TSAKA DA MAGANA AMAJALISAN DATTIJAN AMERICA

Masu zanga-zanga da ke kiran a tsagaita wuta a Gaza sun katse Sakataren Harkokin Wajen Amurka Anthony Blinken a lokacin wani zaman sauraron jin bahasi na Majalisar Dattijai ranar Talata.

Mutane da yawa sun yi cincirindo suna ta kuwwar "A tsagaita wuta yanzu!"

Sakatare Blinken da Sakataren Tsaron Amurka Lloyd Austin na gabatar da jawabi ne game da bukatar fadar White House ta neman amincewa da kudin tsaro dala biliyan 106.

Kudin ya kunshi dala biliyan 14.3 don tallafawa kokarin sojojin Isra'ila a kan kungiyar Hamas.

Suna tsaye daya bayan daya, masu zanga-zangar sun jira har lokacin da Mista Blinken ya fara bayar da bahasi kafin su fara yi masa ihu. Anthony Blinken dai ya dakata yayin da 'yan majalisar ala tilas suka jingine zaman a lokuta da dama.

'Yan sandan da ke kula da ginin majalisar dokokin sun yi hanzari suka rako masu zanga-zangar daga zauren a lokacin da suka fara ihu.

'Yan sanda sun ce an kama mutum 12 saboda yin zanga-zanga ba bisa ka'ida ba a cikin wani sashe na majalisar.

Wasu daga cikin wadanda suka katse zaman majalisar na da alaka da wata kungiya mai adawa da yaki wadda ake kira CODEPINK, ta kuma yi kira ga Amurka ta daina tura makamai Ukraine.

Masu zanga-zangar da dama sun daura kyalle mai rubutu "Ba mu yarda da yi wa Gaza kofar rago ba", daidai lokacin da suke kira ga Amurka ta dakatar da tura wa Isra'ila kudade.

Kungiyar CODEPINK ta tabbatar da cewa an kama wasu daga cikin wakilanta.

Ta ce wasu sun sanya jan fenti a hannuwansu "don nuna alamar jini". Mista Blinken ya yi nuni da masu zanga-zangar a karshen sanarwarsa da cewa, ga kuma "jijiyoyin wuyan da aka tayar a wannan daki".

"Dukkanmu mun dukufa wajen kare fararen hula. Dukkanmu mun san irin wahalhalun da ake ciki a daidai wannan lokaci da muke magana, dukkanmu mun dukufa wajen ganin karshen haka," a cewarsa.

Sai dai ya kara da cewa, abu ne mai muhimmanci ga Amurka ta mara baya ga abokan kawancenta.

Monday, October 30, 2023

LOKACI YAYI DAYA KAMATA ATIKU ABUBAKAR DAN TAKARAR JAM’IYAR ADAWA DAYAKOMA GEFE

Fadar shugaban ƙasar Najeriya ta mayar wa da jagoran adawa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, martani tana mai ba shi shawarar ya "kawo ƙarshen" burinsa na zama shugaban ƙasa.

Martanin na zuwa ne bayan wani taron manema labarai da ya gudanar a yau Litinin, inda ya yi watsi da hukuncin kotun ƙolin da ya jaddada nasarar Shugaba Bola Tinubu na jam'iyyar APC a zaɓen 2023.

Kazalika, Atiku ya ba da shawarar sauya wa'adin mulki zuwa karo ɗaya kuma na shekara shida, da kuma mayar da zaɓe da tattara sakamako ta hanyar latironi su zama tilas a Najeriya.

"....[Atiku] ya mayar da kansa ɗan jagaliya ta hanyar ƙasƙantar da hukumomin ƙasa baki ɗaya don cimma abin da ba zai iya samu ba a akwatin zaɓe," a cewar martanin da Bayo Onanuga - mai taimaka wa shugaban ƙasa kan kafofin yaɗa labarai - ya wallafa a dandalin X.

Ya ƙara da cewa "muna so mu bai wa Atiku shawarar cewa dole ne yanzu ya katse burinsa kuma ya matsa gefe".

Sunday, October 29, 2023

ANHANA MANYAN MOTOCI SHIGA RIGASA

RIGASA

SANARWA  SANARWA SANARWA

Duba da abubuwanda suke gudana da irin barazanarda AL ummar Rigasa ke fuskanta
GA Masu manyan motochi ta Hanyar shigo
Da fetir ko gas ko empty din Mota Wanda suke
Fakin bakin titi da chikin unguwanni. BA bisa
Kaida ba  Wanda Hakan. Ka Iya haifar da gobara  da Hadarin ababen hawa. Da kuka lalata titi

Bisa tattaunawa da Shuwagabanin Qungiyoyin
Direbobi, da Shugabanchin karamar hukumar Igabi, da Hadin guwar masarauta, da hukumar Yan Sanda  da Road safety D kastelia.

AN HARAMTA SHIGOWAR DUK WATA BABBAR
MOTAR MAI KO TA KAYA CHIKIN RIGASA

Sai dai Wacce zata sauke man fetir ko gas a
Gidan man  eyoun ko mobile  ko kamo. Trailer
Kuma  matuqar ba kayan Yan kasuwar Mu na
Rigasa zasu kawo ba suma An Hana,  Amma motar itache Wacce ta dauko itache  zasu Iya
Shigowa  

Akwai  hukumar da aka tanada wayanda zasu
Chigaba da gudanar da Aikin kulawa Don ganin
An gabatar da Wannan doka bisa tsari

Zaa sauke karfen da aka Sanya a Abuja road
Duk Direban da yazo zayyi slow a binchika
Sannan abude masa in Wanda doka ta aminchene ya Shiga

Duk Wanda ya taho da gudu ya karyar karfen
To zaa kama motar har sai an tabbatar da
Ya Gyara dukkan Barnar da yayi

Dafatan zaa kiyaye doka a zauna lafiya Allah ya tsaremu da tsarewarsa amin

SAKON SARKIN KANO ZUWA GA SHUGABAN KASAN NIGERIA

SAKON SARKIN KANO GA SHUGABAN KASA Yau litinin 12/2/2024 Mai martaba sarkin kano Alh Aminu Ado Bayero CFR CNOL JP ya karbi bakuncin matar sh...